Trump zai kori ma'aikatan USAID 1600

Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta sanar da korar ma'aikatan hukumar da ke bai wa kasashen ketare agaji USAID har 1600.

Kazalika, an kuma tilasta wa wasunsu da dama a fadin duniya tafiya hutun dole daga ranar Litinin bayan fara soke ayyukan hukumar da shugaban ya yi.

Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID na shirin rufewa

Wannan matakin shi ne na baya-bayan nan a wani abinda Trump ya ce zai rage yawan kudi da ake kashewa wajen wasu harkokin gwamnati.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne wani alkalin Amurka ya yanke wani hukunci da zai bar gwamnatin Trump ta soke ayyukan ma'aikatan USAID a fadin duniya.

Najeriya za ta dauki nauyin ma'aikatan USAID

Hukumar ta USAID ta ce matakin da gwamnatin na Trump ta dauka zai shafi guraben ayyuka 2000 a kasar ta Amurka kadai.


News Source:   DW (dw.com)