Masu gabatar da kara na tarayya a Amurka sun sake gabatar da wasu sabbin tuhume tuhume a kan Donald Trump game da yunkurinsa na sauya sakamakon zaben shugaban Amurka na 2020 wanda ya sha kaye a hannun Joe Biden
Masu gabatar da karar sun sauya sigar gabatar da karar ce bayan da kotun koli ta yanke hukuncin cewa tsoffin shugabannin kasar suna da rigar kariya daga tuhumar da za ta tozartar da su.
Sabbin tuhume tuhumen da aka takaita zuwa kundi mai shafi 36 na kunshe da tuhuma hudu da aka yi wa Trump tun da farko sai dai an cire wadanda shugaban ke da rigar kariya akansu.