Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya ce idan har ya ci zaben biyar ga watan Nuwamban 2024 zai nada hamshakin attajirin nan na duniya Elon Musk domin ya shugabanci wata hukuma da zai kafa, wacce za ta sanya ido kan tabbatar da gwamnati na aiki yadda ya kamata.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban na Amurka ya tattauna da mataimakansa makonni da suka gabata a kan kafa hukumar da ya ce za ta yi aiki sosai don tabbatar da Amurka ta ci gaba.
Donald Trump ya yi gargadin korar baki idan ya samu mulki
Wannan dai shi ne karon farko da Trump ya bayyana cewa Elon Musk maishafin X wanda a baya ake kira Twitter ya amince da nadin nasa amma idan Trump din ya ci zabe.
Trump zai fuskanci sabbin tuhume tuhume kan zaben 2020
Attajiran biyu sun kulla abota da ake ganin tana kara karfi a baya-bayan nan musamman yadda mista Musk din ke nunawa Trump goyon baya karara.