Shugaba Donald Trump ya zargi Afrika ta Kudu da kwace filaye ba bisa ka'ida ba bayan da Shugaba Cyril Ramaphosa ya saka hannu a kan wata doka da ta tanadi hakan. Trump ya kuma yi barazanar katse duk kudaden da Amurka ka zuba wa Afirka ta Kudu har sai an gudanar da cikakken binciken kan wannan lamari.
A karshen watan Janairu da ya gabata ne dai shugaba Cyril Ramaphosa ya kaddamar da dokar da ta bai wa gwamnati damar kwace wasu filaye galibi mallakin fararen fata ba tare da biyan diyya ba a wani mataki na samar da daidaito da kuma adalci ga 'yan kasar.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana matakin a matsayin wani yunkurin gyaran kura-kurai na rashin daidaito da kasar ta gada daga Turawan mulkin mallakar na Burtaniya.
Sai dai wannan mataki ya gamu da suka daga masu ra'ayin mazan jiya ciki har da attajirin nan Elon Musk dan asalin Afrika ta Kudu wanda ke da kusanci da shugaba Donald Trump.