Trump ya lafta wa ICC takunkumai

Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta takunkumai kan Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC a ranar Alhamis saboda abinda ya kira bincike mara tushe da sahihanci da kotun ke yi kan Amurka da kawarta Isra'ila.

Fadar White House ta fada cewa Trump ya sanya hannu kan dokar shugaban kasa inda ya ce kotun ta birnin Hague ta yi amfani da karfinta ta hanyar da bata dace ba saboda bada umarnin kamo mata Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

Kotu ta samu Trump da laifi amma babu hukunci

Trump ya kuma bayar da umarnin rike kadarori da kuma daura takunkumin tafiye-tafiye kan wasu jami'an kotun da wasu ma'aikatanta da iyalansu da kuma duk wanda ya taimaka wa kotun wajen gudanar da binciken.

Ko da yake ba a bayyana sunayen mutanen da aka kakaba wa takunkuman ba, amma a baya gwamnatin Amurka karkashin Trump ta daura takunkumai kan babban alkalin kotun.

Kotu ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Donald Trump

Amurka da Isra'ila duk ba mambobin kotun duniyar bane, kuma ICC ba ta kai ga mayar da martani kan takunkuman na Trump ba.


News Source:   DW (dw.com)