Trump ya lafta harajin kaso 25% ga karafa dake shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta harajin kaso 25% ga dukkan karafa da dalma da ake shigarwa kasarsa.

Da yake sanya hannu a kan dokar harajin a fadar mulki ta White House, shugaban dan jam'iyyar Republican ya ce harajin zai shafi dukkan kasashe.

Trump ya yi ikirarin cewa matakin babban al'amari ne kuma zai azurta Amurka. Duk kuwa da rashin karin haske a kan yadda hakan zai faru.

China da Kanada da Mexico sun mayar wa Amurka da martanin haraji

Ko da yake da farko gwamnatin Amurka ba ta wallafa takardun dokar ba, sai dai kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa za a fara aiwatar da ita ne a ranar hudu ga watan Maris mai kamawa.

China ta yi karin harajin kashi 15% kan Amurka

Masana tattalin arziki na ganin kakaba haraji ba shi ne mafita ba wajen habaka tattalin arziki amma Trump ya tsaya kai da fata cewa matakan nasa su ne za su sassaita tattalin arzikin na Amurka.


News Source:   DW (dw.com)