Trump ya kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 47

A ranar Litinin ne Donald Trump ya sha rantsuwar zama sabon shugaban kasar Amurka na 47bayan nasarar da ya samu kan 'yar takarar shugabancin kasar ta jam'iyyar Democrats Kamala Harris.

Mista Trump ya yi rantsuwar ce tare da alwashin yin aiki tukuru domin farfado da darajar Amurka a idon 'yan kasa da kuma duniya baki daya.

An gudanar da bikin rantsuwar ce a cikin babban zauren Capitol Rotunda maimakon waje sakamakon sanyi da ake fama da shi.

Karfin ikon shugaban Amurka karkashin tsarin mulki

Mista Trump ya yi alkawarin sanya hannu kan manufofinsa da dama wadanda shugaban kasa ke da ikon amincewa da su a ranar farko ta kama aiki.

Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce daga yanzu kasar za ta amince ne da jinsi kashi biyu kadai wato maza da kuma na mata.

Trump ya sanar da hakan ne a yayin jawabin jim kadan bayan rantsuwar kama aiki.

Shugaban ya ce tsarin ya yi daidai ne da daraja mata da kuma tabbatar da 'yancinsu tunda su ke samar da al'umma ta hanyar haihuwa.

Scholz na Jamus ya jaddada aniyar aiki da Trump na Amurka

Shugaban na Amurka zai iya aiwatar da wasu manufofinsu ta hanyar amfani da dokar karfin ikon shugaban kasa ba tare da jiran sahalewar majalisa ba.

Dama Trump ya sha sukar masu akidar sauya jinsi da kuma masu rajin karesu abinda ya kasance daya daga cikin batutuwa da 'yan adawarsa suka rika sukarsa da shi.


News Source:   DW (dw.com)