Trump ya dauko hanyar lashe zaben Amurka

Republican ta kuma samu gagarumar rinjaye a kujerun majalisar wakilai da ta dattawa a jihohin West Virginia da Ohio. A can kuwa jihohin New York da California Jam'iyyar Democrats ta Kamala Harris na ci gaba da mamaya duk da cewa a tarihin jihohin Republican ce ke lashe kujerun 'yan majalisa.

Karin bayani: Harris na zawarcin kuri'un musulmi a Michigan

A wani labari kuma da ke daukar hankali a siyasar kasar, 'yar takarar majalisar wakilan Amurka musulma dake da tsatso da Larabawan Falasdinu ta Jam'iyyar Democrats Rashida Tlaib, ta lashe zabe a jihar Michigan.

Karin bayani: Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zaben Amurka 

Rashida Tlaib na gaba-gaba wajen sukar manufofin gwamnatin Amurka kan gudummuwar makamai da take bai wa kasar Isra'ila. A shekarar da ta gabata 'yar majalisar ta fuskanci matsin lamba da kuma bincike daga hukumomin Amurka kan furucin da ta yi bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba.

Rashida ta lashe zaben fidda gwani a mazabarta ba tare da hamayya ba kuma ta kada 'dan takarar jam'iyyar Republican James Hooper da ke zawarcin kujerar majalisar wakilan yankin.

 


News Source:   DW (dw.com)