Tun da fari dai hukumomin Amurka sun bukaci kamfanin na Tiktok mallakin kasar China da ya sayar da rukunin kamfanin ga 'yan kasuwan Amurka ko kuma ya fuskanci hukunci mai tsanani da ya hada da toshe kafofin sadarwar kamfanin.
Karin bayani: Trump zai dakatar da TikTok a Amirka
Gwamnatin Trump mai jiran gado ta bukaci sake yin nazari kan haramcin dokar wacce za ta fara aiki a hukumance a ranar 19 ga watan Janairu, kwana guda kafin rantsar da shugaba Donald Trump a ranar 20 ga watan Janairun 2025.
Karin bayani: Tiktok zai kalubalanci dokar shugaba Biden
Kotun kolin Amurka ta sanya ranar 10 ga watan Janairu a matsayin ranar da zata saurari karar da aka shigar gabanta na dakatar da haramcin amfani da TikTok a Amurka. Mutane sama da miliyan 170 ne ke amfani da TikTok a Amurka.