Trump da Macron sun gana a Paris

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugaban mai jiran gado na Amurka, Donald Trump ya kai wajen Amurka tun bayan sake zabensa da aka yi. A ganawarsu gabanin bikin sake bude majami'ar Notre Dame da aka yi wa gyara bayan tashin gobara shekaru biyar din da suka gabata, Donald Trump ya ce a bayyana take cewa duniya na cikin wani yanayi na rudani, yana mai cewa za su tattauna batun a wannan lokaci.

Karin bayani: Trump da Macron sun halarci ranar D-Day

Duk da 'yar tsamar da ke tsakanin shugabanin biyu a zamanin mulkin Mista Donald Trump na farko, shugaban na Amurka ya yaba wa alakar da ke tsakaninsa da Emmanuel Macron. Daga nashi bangare, Shugaba Macron ya ce halartar bikin da Trump ya yi, wata karramawa ce ga Faransawa kasancewar majami'ar ta kone ne a lokacin mulkin shi Trump na farko. Ana dai sa ran bangarorin biyu za su tattauna a kan batutuwan yake-yaken Ukraine da kuma na Gabas ta Tsakiya da ma batun kasuwanci.

 


News Source:   DW (dw.com)