TikTok ya fara daina aiki a Amurka

Ma'abota manhajar kimanin miliyan 170 a Amurka sun yi ta samun sakonnin cewa, an dakatar da manhajar na dan wani lokaci. Dama TikTok din ya bayyana cewa zai daina aiki a Amirka daga wannan Lahadin idan har gwamnatin Shugaba Joe Biden ba ta dauki matakin hana dakatar da shi ba. Amirkar dai ta ce za ta dauki matakin dakatar da manhajar idan har kamfanin ByteDance mallakin manhajar ya ki siyar wa Amurka.

Sai dai shugaba mai jiran gado, Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta ganin ya kara wa'adi gabanin dakatarwar. Mista Trump ya ce akwai yiwuwar ya kara tsawaita amfani da manhajar zuwa kwanaki 90 idan ya sha rantsuwar kama aiki.

Karin bayani: Trump ya bukaci jinkirta haramcin amfani da TikTok

A watan Afirilun bara ne dai, shugaba Joe Biden ya yanke hukuncin hana amfani da manhajar ko siyar da ita, wanda majalisar dokokin kasar ta amince da shi bisa dalilai na tsaro, inda 'yan majalisar ke fargabar China ka iya amfani da manhajar wajen samun bayanan Amirkawa domin ta yi amfani da su wajen yada manufofinta na siyasa.

 


News Source:   DW (dw.com)