Tawagar Amirka na ziyarar Kenya

Tawagar Amirka na ziyarar Kenya
Tawagar Amirka na ziyara a Kenya a daidai lokacin da kasar ke cikin rudani bayan fitar da sakamakon zaben da ya bai wa William Ruto nasara.

Wata tawagar Amirka ta isa kasar Kenya inda jami'an gwamnatin ke shirin ganawa da zababben shugaban kasar William Ruto. Ziyarar na zuwa a daidai lokacin da abokin takararsa da ya sha kayi a zaben Raila Odinga ke shirin shigar da kara a gaban kotu don kalubalantar sakamakon zaben.

Jakadiyar Amirka a Kenya Meg Whitman ta ce, tawagar za ta kuma gana da Shugaba Uhuru Kenyatta daga bisani, Kenyatta da ya nuna goyon bayansa ga Odinga, bai ce ko uffan ba tun bayan fitar da sakamakon zaben da mataimakinsa William Ruto ya lashe da yar tazara, akwai yiyuwar ya tabo batun zaben a yayin wannan ganawar. 

Zaben kasar Kenyan nada matukar  tasiri a yankin kahon Afirka ganin yadda aka zauna lafiya a kasar da a baya ta sha fama da rikicin bayan zabe da ya lakume rayuka da dama, baya ga haka Shugaba Kenyatta na da karfin fada a ji, musanman ganin yadda ya ke aiki tare da taimakon Amirka na shiga tsakani a kokarin samar da maslaha a rikicin kasar Habasha.
 


News Source:   DW (dw.com)