Tattalin arziki Faransa da ke cikin mawuyacin hali zai smau bunkasa na kaso 0.2 cikin 100 a farkon shekara mai zuwa ta 2025, duk da matsalolin takun saka na siyasa da kasar ta samu kanta game da amincewa da kasafin kudin shekarar badi.
Karin Bayani: Faransa ta yi sabon Firanminista
Hukumar kula da kididdiga ta kasar ta bayyana haka a wannan Talata. Ita dai Faransa tana cikin rudanin siyasa inda majalisar dokoki ta kada kuri'ar yankar kauna ga firaministan kasar game da rikicin kasafin kudi.