Taron tattaunawar kawo karshen yakin Rasha da Ukraine

Manyan jami'an diflomasiyya na kasdashen Amurka da Rasha sun gana a wannan Talata a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, a matakin farko na tattaunawa domin kawo karshen kusten Rasha kan kasar Ukraine. An yi ganawar tsakanin Marco Rubio sakataren harkokin wajen Amurka da kuma Sergei Lavrov ministan harkokin wajen Rasha.

Karin Bayani: Taron tsaro na shekara-shekara a Jamus

Saudiyya | Ganawa tsakanin Amurka da RashaManyan jami'an Rasha´da AmurkaHoto: Artyom Popov/TASS/dpa/picture alliance

Tawogar kasashen biyu ta kuma kunshi manyan jama'ai da suke cikin shirin tattaunawar. Sai dai akwai damuwa daga kasashen Turai wadanda ba sa cikin wadanda aka gayyata a wajen taron.

Yayin da ake wannan ganawar rahotanni daga birnin Moscow na Rasha sun bayyana cewa Shugaban kasra Vladimir Putin yana shirye da tattaunawa da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, domin warware yakin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu.

 


News Source:   DW (dw.com)