Kungiyar kwadago ta duniya ILO ta baiyana fargabar cewa fasahar kirkira ta AI na iya haifar da wagegen gibi da rashin daidaito a tsakanin jinsi sabanin shafe guraben aiki da ake tsammani.
Shugaban kungiyar kwadagon ta duniya Gilbert Houngbo ya baiyana haka a birnin Paris a taron koli kan fasahar kirkira da ya sami halartar shugabannin kasashe da shugabannin cibiyoyi da kamfanonin fasaha na duniya.
Manufar taron wanda shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban Indiya Narendra Modi ke karbar bakuncinsa shi ne shimfida ginshikin gudanarwa ga sabon bigiren yayin da manyan kasashe da kamfanoni suka fara rige-rigen zama ja gaba a fannin fasahar da ke bunkasa cikin hanzari.
A halin da ake ciki dai yanzu fasahar ta AI na neman maye gurbin dan Adam a wasu bangarori na ayyuka kamar na akawu da kuma sakatarori, aikin da galibi mata ke gudanarwa a cewar Gilbert Houngbo shugaban kungiyar kwadago ta duniya.
Shugabannin kasashe da manyan jami'an gwamnati da shugabannin kamfanoni da masana kimiyya daga kasashe kimanin dari daya suke halartar taron na kwanaki biyu da aka fara a wannan litinin din.