Muhimmin batu a taron kolin shugabannin shi ne karfafa makaman kariyar sararin samaniya domin fatattakar sojojin Rasha daga birane da iyakokin turai kamar yadda Zelenskyy ya wallafa a shafin sada zumunta na X gabanin taron.
Taron dai na kasancewa na karshe gabanin zababben shugaban Amurka Donald Trump ya karbi ragamar mulki a ranar 20 ga watan Janairu.
Makasudin taron shi ne domin hanzarta samar wa Kiev karin tallafi saboda Trump ya nuna cewa ba lallai ba ne ya ci gaba da tallafa wa Ukraine kamar yadda shugaba Joe Biden ya yi.
Firaministan Italiya Giorgia Meloni ta ce dukkan aminan kasashe suna fata Trump ya daidaita diflomasiyya da barazanar da ya ke yi a hannu guda, kada ya ce zai yi watsi da Ukraine.