Taron kasahen G7 kan Isra'ila

 Ministocinza su  tattauna kan sammacin kama Benjamin Netanyahu da Mohammed Deif na Hamas  da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar, kamar yadda firaministan Italiya Giorgia Meloni ta sanar. Wannan sanarwa na zuwa ne, bayan maganganu masu cin karo da juna daga ministoci guda biyu na firaministar. Yayin da Ministan Tsaro Guido Crosetto ya tabbatar da cewa Italiya za ta  kama Netanyahu da ministansa na tsaro  Gallant idan sun zo Italiyar. Mataimakin firaministan kasar Matteo Salvini, na jam'iyyar masu adawa da 'yan cirani kuma abokan kawance na gwamnatin, ya ce suna  yin maraba da Netanyahu idan ya zo  Italiya.


News Source:   DW (dw.com)