Taron G7 ya yi wa Ukraine alkawari

Taron G7 ya yi wa Ukraine alkawari
Kasashe bakwai mafiya karfin masana'antu na duniya sun yi alkawarin dorewa kan aniyarsu ta taimaka wa Ukraine, kasar da a yanzu ke fama da mamaya daga Rasha.

Shugabannin kasashen wadanda ke taro a kudancin Jamus, sun alkawarin sama wa Ukraine kudaden da suka kai euro bilyan 29 da milayan 500 domin ba ta damar cike gibin kudade da ta samu.

Kasar Amirka musamman ta yi alkawarin bai wa Ukraine makamai masu iya kakkabo makami mai linzami mai cin dogon zango, da makaman atilare gami da na'urorin gani kwa-kwaf daga nesa.

Kasashen bakwai mafiya karfin tattalin arziki sun sha alwashin ci gaba da tsananta wa Rasha har sai ta kawo karshen yakin da ta ke yi a Ukraine.

Sai kuma bukatarsu ga Rasha da ta dakatar da hare-hare domin ba da damar wucewarsu kayan abinci saboda amfanin kasashen duniya.


News Source:   DW (dw.com)