'Yan majalisar dokokin Tarayyar Turai, sun yi kiran da a janye haramcin da aka dora wa Ukraine na amfani da makaman yaki da kasashen yammacin duniya suka samar mata, makaman da aka tsara kasar za ta yi amfani da su a kan wasu yankuna na Rasha.
Matakin dai ya dakatar da Ukraine din ne daga samun sukunin kare kanta yadda ya dace daga hare-haren Rasha da ke shafar al'uma da kuma muhimman gine-ginen kasar, a cewar majalisar dokokin ta Turai.
Kuduri ne dai da ya samu goyon baya daga 'yan majalisar EU su 425, a taron da suka yi a Strasbourg na kasar Faransa, inda 131 suka kasance wadanda suka bijire wa bukatar, wasu mutum 63 kuwa ba halarci zaman ba.
Zaman majalisar ya kuma bukaci da a tsawaita wa'adin dora wa Rasha da kawayenta takunkumai na karya tattalin arziki kan mamayar da ta yi wa Ukraine.