Tanzaniya: Dan adawa da aka sace ya samu munanan raunuka

Jam'iyyar ACT Wazalendo da ke adawa a Tanzaniya ta sanar da samun shugabanta na reshen matasa a bakin teku dauke da munana raunuka bayan da aka sace shi, lamarin da ke nuna cewar an lakaba masa mummunan duka. Ita dai jam'iyyar da ke fafutukar neman sauyi ta zargi jami'an tsaro da yin garkuwa da Abdul Nondo bayan bacewarsa tun a ranar Lahadi a kusa da Dar es Salaam da ke zama cibiyar kasuwancin kasar. Sai dai sanarwa da 'yan sandan suka fitar, ta nuna cewar Abdul Nondo ya je hedikwatar jam’iyyarsa ne bayan da wadanda suka yi garkuwa da shi suka ajiye shi a bakin tekun Coco, sannan aka kai shi asibiti daga bisani domin duba lafiyarsa.

Karin bayani: 'Yan adawa na fargabar salon mulkin danniya a Tanzaniya

A watannin baya-bayan nan dai, jam’iyyun adawa sun sha yin Allah wadai da sace 'ya'yansu da ake yawan yi, bayan da shugaba Samia Suluhu Hassan ta rungumin tsarin mulkin tursasa wa 'yan adawa da wanda ya gabace ta John Magufuli ya yi kaurin suna a kai. ko a ranar zaben kananan hukumomi a ranar Laraba da ta gabata, sai dai babbar jam’iyyar adawa ta Chadema ta yi tir da kisan da aka yi wa mambobinta biyu, tare da zargin gwamnatin Tanzaniya da magudi a zabe a karkashin jam'iyya Chama Cha Mapinduzi (CCM) da ke mulki.

 


News Source:   DW (dw.com)