Tankiya a tsakanin Amirka da Chaina

Tankiya a tsakanin Amirka da Chaina
Shugabar Majalisar Wakilan kasar Amirka Nancy Pelosi ta ci gaba da karyata zargin kai ziyara Taiwan da niyyar tayar da zaune tsaye.

Shugabar Majalisar Wakilan kasar Amirka Nancy Pelosi ta ce, ba ta kai ziyara tsibirin Taiwan da niyyar tayar da zaune tsaye ba, kalaman nata sun biyo bayan kurar da ziyarar ta tayar, ziyarar da ta fusata Chaina, har ta soma wani atisayen soja da ba a taba ganin irinsa ba tare da harba wasu makamai masu linzami a cikin tekun da ke kusa da makwabciyarta Taiwan dama yi wa tsibirin kawanya a wannan Jumma'ar.

Amirka ta jadadda goyon baya ga Taiwan, da a yanzu haka, ke fuskantar barazanar soji daga Chainan. A farkon wannan makon ne, Nancy Pelosi ta soma rangadi a wasu kasashen yankin Asiya, amma ziyarar da ta kai Taiwan, wanda shi ne karon farko a cikin shekaru ashirin da biyar da wani babban jami'in Amirka ke ziyarar  Taiwan, tsibirin da mahukuntan Beijing ke wa kallo a matsayin wani lardin kasar da ya balle, ya bar baya da kura.
 


News Source:   DW (dw.com)