Kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahida ya zargi Bennett da yada wasu manufofi da ba su gane musu ba a cikin Afghanistan. A cikin sanarwar da ya fitar, Bennett ya bukaci gwamnatin Taliban ta janye matakin nata, kana ya ce zai ci gaba da gudanar da aikinsa daga wajen kasar. A baya-bayan nan ne dai, Bennett ya ce yadda Taliban ke tafiyar da rayuwar mata da 'yan mata a kasar laifi ne na cin zarafin bil Adama.
Tun dai a shekarar 2022, Majalisar Dinkin Duniya ta nada Benett a matsayin babban mai binciken, shekara guda bayan da Taliban ta sake kwace ragamar mulkin kasar.