Takun saka tsakanin gwamnatin Pakistan da 'yan adawa

Takun saka tsakanin gwamnatin Pakistan da 'yan adawa
An shiga dambaruwar siyasa kan batun tuhumar tsohon Firaminista Imran Khan na Pakistan wadda gwamnati take zargi da zagon kasa.

'Yan adawa na kasar Pakistan sun yi gargadi kan yuwuwar kama tsohon Firaminista Imran Khan wanda ake neman tuhuma karkashin dokokin yaki da ta'addanci.

Tun bayan tunbuke shi kan madafun iko a watan Afrilu, tsohon Firaminista Imran Khan yake gangami a sassan kasar inda ake ganin yana zagon kasa ga gwamnatin Firaminista Shehbaz Sharif.

A wannan Litinin akwai akwai kimanin magoyan bayan tsohon firaministan 500 suka yi gangami a gefen gidansa da ke unguwar masu hannu da shuni a Islamabad babban birnin kasar ta Pakistan.

Yanzu haka 'yan sanda sun shigar da tuhumar bisa ta'addanci a kan tsohon tsohon Firaminista Imran Khan lamarin da ya kara zaman tankiya na siyasa a kasar.

 


News Source:   DW (dw.com)