Taiwan ta sha alwashin kare kanta daga China

Taiwan ta sha alwashin kare kanta daga China
Sojojin China sun harba makami mai linzami bayan atisayen soji a kusa da Taiwan, a wani mataki na gargadi tare da hana yuwar tasirin Amirka na tabbatar da 'yancin tsibirin a ziyarar Nancy Pelosi.

Taiwan ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen kare yankinta daga dukkannin wata barazanar soji da Chaina ke mata. Shugaban tsibirin yankin mai cike da takkadama wacce kuma Beijin ke dauka a matsayin yankinta, ya ce matakin da Sin ta dauka na kaddamar da atisayen soji a kewayen Taiwan ya saba 'yancin kasa da kasa tare da haifar da nakaso ga harkokin kasuwancin duniya yadda ya kamata.

Sai dai Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi kakkausar suka kan matakin da ministocin kasashen kungiyar G7 suka dauka kan lamarin.

"Gargadin da ministocin harkokin wajen na G7 na sa mutane suna jin cewa ba su da tushe, Amirka ce ummul aba'isin tashin hankali da ake ciki yanzu a mashigin Taiwan. Amma Washington ta yi watsi da kakkausar murya na adawar kasar Sin da kuma wakilci mai girma, ta amince da ziyarar da mutum na uku a gwamnatin Amirka ta kai yankin Taiwan. Wannan babban lamari ne da ke kara lalata dangantakar Amirka da Taiwan, kuma yana yin illa sosai ga tsarin Sin daya tilo."


News Source:   DW (dw.com)