Tagwayen hare-haren ta'addanci

Tagwayen hare-haren ta'addanci
Rahotanni daga kasar Burkina Faso na nuni da cewa an halaka mutane 15 ciki har da sojojin kasar tara sakamakon wasu tagwayen hare-hare da 'yan ta'adda suka kai wa dakarun kasar.

Rundunar tsaron kasar Burkina faso ta ce an kai hare-haren a wasu sansanonin sojin kasar biyu da ke Gaskindé da Pobe Mengao a yankin arewci, kana kuma wasu fararen hula hudu da 'yan kato da gora biyu na daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu a cikin harin.

Sanarwar ma'aikatar tsaron ta ce an kuma samu akalla mutnane 30 da suka jikkata a jerin hare-haren na wanda 'yan ta'adda da ya auku a kusa da iyaka da Mali. Tun a shekarun 2015 ne kasar Burka Faso mai iyaka da Mali da Jamhuriyar Nijar ke fuskantar hare-haren 'yan ta'adda wanda kuma ya yi sadanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da fararen hula musamman a yan,kin arewacin kasar.


News Source:   DW (dw.com)