A ranar Asabar ne dai rahotanni suka tabbatar da cewa mayakan da ke jayayya da gwamnatin ta Syria sun kwace iko da kusan ilahirin birnin Aleppo, wanda ke na biyu mafi girma a kasar.
Gamayyar kungiyoyin tawaye karkashin inuwar kungiyar Hayat Tahrir al-Sham, su ne suka gama karfi wajen fatattakar mahukunta ciki har da kwamandojin yakin gwamnati daga birnin.
Sama da mutum 300 ne da suka hada da fararen hula suka mutu, tun bayan barkewar sabon artabu a ranar Laraba, kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin 'yan Syria wato Syrian Observatory for Human Rights ta tabbatar.
Kasar Rasha da ke taimaka wa Syria a yakin da take yi, ta ce ta aika da wasu jirage domin taimakawa wajen yaki da mayakan na tawaye a kasar.