Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Switzerland ita ce ta sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai a AFP, ta kara da cewa an kuma gayyaci dukkanin kasashe 196 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kare hakkin 'dan adam ta Geneva.
Karin bayani: Matakin karshe na musayan fursunoni tsakanin Hamas da Isra'ila.
Babu wani mataki da aka dauka kan yakin na Hamas da Isra'ila tun daga lokacin da kasashe 15 na Kwamitin Sulhu na MDD suka amince da daftarin tsagaita bude wuta a Gaza, har dai zuwa lokacin da aka fara aiwatar da yarjejeniyar musayar fursunoni da gawarwaki tsakanin Isra'ila da Hamas.
Karin bayani: Kasashen Larabawa na adawa da kwace Gaza
Tun dai a watan Satumbar 2024, Kwamitin Sulhu na MDD ya bukaci kasar Switzerland da ta jagoranci taron tattaunawa kan batun kare hakkin al'ummar Gaza.