Jam'iyyar Social Democrat ta Sweden ta dade tana adawa da shiga NATO, inda take waswasin kar ta fada tsaka mai wuya, amma jami'iyyar ta cimma matsayar sake duba manufofinta.
Wannan dai na zuwa ne bayan tuni kasar jam'iyyar Social Democrat a Finland ta sanar da goyon bayanta ga shiga NATO a ranar Alhamis da ta gabata. Matakin da tuni kasar Rasha ta yi fara nuna 'yar yatsa. A halin da ake ciki, Zelenskyy na Ukraine ya rattaba hannu kan wata doka ta haramtawa jam'iyyun da ke goyon bayan Rasha.