Wannan mataki ya fara sa wasu kashen waje fara nuna tababa kan makomar kasar da ta sha fama da tashe-tashen hankula a shekarun baya.
Amma gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce sun dauki matakin tsawaita mulkin rikon kwarya ne zuwa 2024 don tinkarar kalubalen da ke hana kasar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2018 na kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekaru biyar ana yi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 400,000.