
Jaridun kasar ta Sudan sun ce kimanin mutum 125 ne hukumomi suka sako bayan umurnin da al-Burhan wanda ke rike da shugabancin kasar ya bayar a yammacin ranar Lahadi.
Shugaban rundunar sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya janye dokar-ta-baci da sojojin kasar suka sanya a lokacin juyin mulkin da aka yi a kasar a shekarar da ta gabata. Al-Burhan ya kuma umurci a sako fursunonin siyasa da ake tsare da su a kasar.
A ranar Asabar da ta gabata MDD ta yi kira ga mahukuntan Sudan da su janye dokar-ta-bacin bayan mutuwar wasu masu zanga-zanga guda biyu a birnin Khartoum.
News Source: DW (dw.com)