Stoltenberg zai karbi shugabancin taron tsaron Munich

Sakataren kungiyar tsaron NATO mai barin gado, Jens Stoltenberg zai zama shugaban majalisar gudanarwar taron tsaro na birnin Munich da ke Jamus. Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya tabbatar da haka daga majiyoyi da dama masu tushe. Kawo yanzu ba a tabbatar da haka a hukumance ba, inda majalisar shirya taron tsaron ta Munich ta ce bisa manufa ba za ta ce komai ba, sai dai mutum ya tabbatar da kansa bisa duk wani abin da ya shafe shi.

A watan Fabrairun shekara mai zuwa ta 2025 ake sa ran Stoltenberg zai karbi ragamar tafiyar da taron tsaron na Munich da ke Jamus, kuma taron tsaro mafi girma a duniya da ke hada masu kula da manufofin tsaro na kasashen duniya. Yanzu haka Christoph Heusgen tsohon jakadan Jamus a Majalisar Dinkin Duniya ke rike da shugabancin taron tsaron.

Shi dai Jens Stoltenberg da zai jagoranci taron tsaron yanzu haka shi ne sakataren kungiyar tsaron NATO mai barin gado, kana tsohon firaministan kasar Norway.

 


News Source:   DW (dw.com)