Steinmeier ya nemi afuwa kan laifukan Nazi

Shugaban kasar Jamus Walter Steinmeier ya nemi afuwar al'ummar Kandanos da ke tsibirin Girka game da laifukan da 'yan Nazi suka aikata musu a lokacin yakin duniya na biyu.

Steimeier ya nemi afuwar ce a lokacin da ya kai ziyara kauyen a ziyara ta farko da wani shugaban kasar Jamus ya kai zuwa yankin.

'Yan Nazi sun afkawa al'umar kauyen da ke tsibirin Crete suka kone shi kurumus a lokacin yakin a ranar 3 ga watan Yuni 1941 a matsayin ramuwar gayya kan kisan Jamusawa sojojin Lema su 25 da mutanen kauyen suka yi yayin da suka nuna turjiya ga Jamusawan.

Yankin na Crete na daga cikin kauyuka kimanin 120 da 'yan Nazi suka murkushe a lokacin yakin duniya na biyu.

 


News Source:   DW (dw.com)