Sri Lanka: Shugaban kasa na riko ya sa dokar ta baci

Sri Lanka: Shugaban kasa na riko ya sa dokar ta baci
Gwamnatin Sri Lanka ta kafa dokar ta ba ci don kawar da shirin haddasa rikici gabannin zaben sabon shugaban kasa a majalisar dokoki a karshen wannan mako.

Rahotanni daga Colombo babban binrin kasar Sri Lanka, na cewa an wayi gari shuru da takaita zirga-zirga a kan titunan binrin.  Tun dai a watan Afirilu, tsohon Shugaban kasar Sri Lanka da ya tsere bayan da 'yan kasar suka mamaye fadarsa, ke sanya dokar ta baci don rage tasirin zanga-zangar tir da gwamnatinsa kan tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.

A ranar Asabar mai zuwa ne majalisar dokokin kasar Sri Lanka za ta gana don fara aikin zaben sabon shugaban kasa, Sri Lanka dai ta roki asusun bada lamuni na duniya da ya samar da agajin gaggawa, amma rudanin siyasa ya kawo tsaiko a tattaunawar.


News Source:   DW (dw.com)