Da ma dai tun kafin rikicin, jam'iyyar adawa mafi girma a kasar ta ce ba za ta shiga cikin gwamnatin da Rajapaksa ke jagoranta ba. Murabus din firaministan dai, na nufin an rushe majalisar ministocin kasar kai tsaye.
A ranar Litinin ne rikici mafi girma ya kaure a kasar lokacin da magoya bayan iyalan Rajapaksa suka yi ta kai farmaki, 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da fesa ruwan zafi. An kuma ayyana dokar ta-baci nan take a garin Colombo, wanda daga bisani aka fadada har zuwa daukacin tsibirin na kudancin Asiya mai mutane miliyan 22.
Kasar Sri Lanka ta yi fama da matsalar karancin abinci da magunguna da mai na tsawon watanni, matakin da ya kara tsananta matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki tun bayan samun 'yancin kai.