Zaben da ke tafe bayan jinkiri na kusan shekara guda da aka samu, za a fafata ne a tsakanin shugaba mai barin gado Mohammad Abdullahi Mohamed Farmanjo da kuma firaminista Mohamed Hussein Roble.
Kasashen duniya gami da kungiyoyi sun taimaka wajen ganin an gudanar da zabe a kasar ta Somaliya da ke fama da matsaloli ko baya ga na siyasa da ma na ayyukan kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai.
Ana fatan wannan zabe da ke tafe ya kawo karshen rigingimu da kasar ke fama da shi musamman na baya-bayan nan hare-haren mayakan Al-shabab da suka kai ga rasa wasu 'yan siyasa biyu.