Sojojin Sudan na kara samun galaba a kan dakarun RSF

A cewar sanarwa da suka fidda bayan kwashe makwanni ana gumurzu sun kwace wasu yankunan da dama na birnin daga hannun sojojin RSF.

Wata majiya ta sojojin gwamntin ta ce dakarun Sudan na kara tunkarar yankunan da sojojin Mohammed Hamdan Daglo suka kafa shinge.

Ko a makon da ya gabata shugaban sojojin sa kai na RSF ya bayyana irin koma bayan da suke samu a yakin da suke gwabzawa da sojojin gwamnati.

Rikicin shugabanci da ya barke a tsakanin bangarorin biyu tun a watan Afrilun 2023 ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar salwantan rayukan dubban fararen hula tare da raba wasunsu da matsugunansu.

 

Karin Bayani: Yan tawayen RSF a Sudan sun kashe akalla mutum 60 a Omdurman  


News Source:   DW (dw.com)