Sojojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram 34

Sojojin Najeriya sun sanar da halaka mayakan Boko Haram 34 a wani artabu a jihar Borno dake Arewa maso gabashin kasar, suma sojin an kashe musu dakaru shida.

An yi arangama tsakanin bangarorin biyu ne a ranar Asabar a kauyen Sabon Gari a yayin da 'ya'yan Boko Haram suka yi wa sojoji kwanton bauna a lokacin da suke komawa sansaninsu.

Najeriya: 'Yan Boko Haram 129,417 sun mika wuya

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Janar  Edward Buba ya ce maharan 'ya'yan ISWAP ne kuma suna amfani da babura wajen hayewa kan duwatsun da ke yankin baya ga amfani da motocin da aka dasa bindigogi a kansu.

Sojojin tare da hadin gwiwar 'yan sakai na Civilian JTF sun dakile harin tare da korar sauran maharan a cewar mai magana da yawun sojin.

An kashe gomman 'yan Boko Haram a Najeriya

Najeriya ta shafe shekara 16 ta na yaki da mayakan Boko Haram a Arewa maso gabashin kasar, rikicin da ya lakume rayukan dimbin fararen hula.


News Source:   DW (dw.com)