Rundunar sojin Najeriya ta hallaka 'yan bindiga kusan 80 a cikin makon da ya gabata. ta sanar da haka ne a ranar Jumu'a, inda mai magana da yawunta Manjo Janar Edward Buba ya fitar da sanarwa yana mai cewa sabon samame da dakarunsu suka kadamar a sassan Najeriya dabam-dabam ya kai ga kama mutum 252 wadanda ake zargi da aikata munanan laifukada kuma kubutar da mutum 67 daga hannun masu garkuwa da mutane.
Hira da Janar Christopher Musa
To view this video please enable JavaScript, and consider upgrading to a web browser that supports HTML5 video
06:48Cikin mutanen da aka kama akwai guda 28 da ake zargi da kwarewa wajen satar danyan man fetur a kudancin kasar, wanda ya dauki dogon lokaci yana haddasa wa Najeriya babbar asara a kudaden shigar da take samu.