Sojojin Mali sun kashe 'yan ta'addan GSIM

Sojojin Mali sun kashe 'yan ta'addan GSIM
Rundunar sojin kasar Mali ta tabbatar da kashe wasu 'yan ta'adda 12 a wani hari ta sama da ta kaddammar a tsakiyar kasar da ke yankin Sahel.

Sanarwar da shugaban rundunar sojin Mali ya fitar ta ce dakarun sun kaddamar da hare-hare biyu ne a ranar Alhamis din da ta gabata a dajin Ganguel, kilo mita 10 daga kauyen Moura da nufin kakkabe gomman 'yan ta'addan da ke dajin. Sanarwar ta kuma ce harin ya karya lagon babbar kungiyar da ke fafatukar jihadi a yankin Sahel ta GSIM.

Rundunar sojin Mali  ta ce ta mayar da martani kan wasu kwararan bayanai da ta samu kan cewa wata kungiyar 'yan ta'adda za ta karfafa wa mayakan GSIM bayan mummunan komabayan da suka samu a yankin Moura. Kasar Mali dai ta sha fama da matsalolin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai tun a shekarar 2012 wanda suka yi sanadiyar mutuwar dubban mutane yayin da wasu dubbai suka rasa matsugunnasu.


      
 


News Source:   DW (dw.com)