Sojojin Jamus za su koma Bosniya

Sojojin Jamus za su koma Bosniya
A karon farko cikin shekaru goma, Jamus ta share hanyar tura sojoji tare da tawagar wanzar da zaman lafiya na EU zuwa Bosniya a wani mataki na shirin ko ta kwana na dakile barazanar Rasha a yammacin Balkans.

Duk da cewa akwai tazara mai yawa tsakanin da Ukraine, amma kasar na fuskantar wani yunkuri na 'yan aware daga  Sabiyawan Bosnia wanda manazarta ke zargin suna samun goyon baya daga Moscow.

Kwanaki kadan bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, EU ta yanke shawarar ninka yawan rundunarta ta EUFOR daga 600 zuwa 1,100 don tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnati a Berlin ta amince da samar da dakaru 50 ga EUFOR zuwa Bosniya, bayan janye sojojinta a karshen 2012, sai dai matakin na jiran hukuncin karshe daga majalisar dokoki ta Bundestarg.


News Source:   DW (dw.com)