Kungiyar ta kafa hujja ce da wani mummunar hari da wata kungiya da ke da alaka da al-Qaida ta kai lardin tsakiyar kasar ta Burkina Faso a watan Augustan shekara ta 2024, da ya halaka wasu mutanen karkara sama da 100. Wata mai bincike kan al'amuran da suka shafi tsaro a yankin Sahel, Ilaria Allegrozzi, ta ce harin da mayakan suka kai kauyen na Barsalogho da ke da nisan mile 50 daga babban birnin Ouagadougou na daya daga cikin misalan irin hadarin da sojojin ke jefe fararen hula.
Karin bayani:'Yan ta'adda sun kashe mutane 10 a Manni na Burkina Faso
Kusan rabin lardunan kasar ta Burkina Faso na hannun kungiyoyin da ke dauke da makamai da ke ikirarin jihadi irin su al-Qaida da IS wanda hare-haren da suke kai wa babu kakkautawa ya raba mutane sama da miliyan biyu da muhallansu, yayin da wasu dubban suka rasa rayukansu.
Karin bayani: Burkina Faso: Zaman makoki bayan harin ta'addanci
Gwamnatin mulkin sojin a nata bangaren ta bakin ministan shari'ar kasar Edasso Rodrigue Bayala, ta musanta rahoton na Human Rights Watch na zargin jefe rayuwar fararen hula cikin garari har ma da zargin tilastawa matasa da yara kanana shiga kungiyoyin sa-kai da ke taimakawa sojojin wajen tabbatar da tsaron kasa.