Sojoji sun sa dokar hana fita a Iraki

Sojoji sun sa dokar hana fita a Iraki
Jami'an tsaro a Iraki, sun kafa dokar hana fita daga karfe uku da rabi na yamma, bayan da magoya bayan Moqtada al-Sadr sun kutsa fadar gwamnati saboda ya sanar da barin harkokin siyasa tare da rufe cibiyoyinsa a kasar.

Malamin mai karfin iko a kasar Iraki, ya jingine harkokin siyasa a wani mataki na mayar da maratani kan dambarwar siyasar kasar. Sai dai ana ganin matakin zai sake mayar da hannun agogo baya kan halin da ake ciki.

A baya dai Sadr ya janye daga harkokin siyasa tare da tarwatsa mayakan sa-kai da ke masa biyayya, amma ya janye 'yan majalisarsa bayan jam'iyyarsa ta zo na daya a zaben da aka yi a watan Oktoba inda ya yi barazanar fitar da 'yan Shi'a masu karfi da ke kusa da Iran.

A baya-bayan nan magoya bayan fitaccen malamin sun kutsa cikin majalisar dokoki da ke birnin Bagadaza, a wani mataki na matsawa gwamnati lamba ta shirya sabon zabe.


News Source:   DW (dw.com)