Sojin Guinea za su yi shekaru 3 a mulki

Sojin Guinea za su yi shekaru 3 a mulki
Sojojin da ke rike da mulki a Guines sun ce an kawo musu shawarar mika mulki cikin watanni 18 zuwa 52. Sai dai wasu 'yan fafutuka sun yi watsi da kudurin, suna masu cewa ba a tuntube su ba.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Guinea Kanar Mamady Doumbouya ya sanar da cewa sun tsayar da wa'adin watanni 39, ya zama tsawon lokacin da sojoji za su mika mulki ga farar hula a kasar. A jawabinsa na kafar talabijin din kasar a yammacin ranar Asabar, Doumbouya ya ce zai mika wa majalisar kasar wannan kuduri domin ta tabbatar da shi. 


Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, ko CEDEAO ta bai wa sojojin  na Guinea Litinin din da ta gabata a matsayin rana ta karshe da ko dai su sanya ranar zabe ko kuma kungiyar ta sanya musu takunkumin karya tattalin arzikin. Sai dai sojojin na birnin Conkry sun bai wa ECOWAS din hakuri, inda suka nemi karin lokaci don kammala tuntuba.


News Source:   DW (dw.com)