Soji a Mali sun kama turawa 'yan ta'adda

Soji a Mali sun kama turawa 'yan ta'adda
A wani farmakin da ta kai kan wasu 'yan kungiyar jihadi, rundunar sojin Mali ta tabbatar da kama wasu mutane biyar da take zargi da hannu a ayyukan ta'addanci.

A cewar rundunar da ta shirya kai farmakin, uku daga cikinsu turawa ne. Ko da yake a cikin sanarwar da rundunar ta fitar bata bayar da cikakken bayanai dangane da mutanen da ta kama a yankin Diabaly ba, kilo mita 300 daga Bamako babban birnin kasar.

Kasar Mali dai da ke karkashin ikon soji a yanzu ta fada cikin rikicin siyasa tun a shekarar 2012, yayin da matsalar kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai da ta ke fama da su ya watsu zuwa makwaftanta Nijar da Burkina Faso.


News Source:   DW (dw.com)