Sojan mai suna Sgt. Vadim Shishimarin yana da shekaru 23, na fuskantar hukuncin daurin rai da rai idan kotu ta same shi da laifukan da ake tuhumarsa na bindige fararen hula a Ukraine a ranar 28 ga watan Febrairu na 2022.
Rasha ta yi ikirarin cewa mayakan Azovstal na Ukraine 771 sun mika wuya a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda ya kawo jimillar wadanda suka ajiye makaman tun ranar Litinin zuwa fiye da 1,700. Amma Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya ce Ukraine ta kuduri aniyar kwato yankunan kudancin kasar da sojojin Rasha suka mamaye.