Siriya ta yi luguden wuta kan 'yan tawaye

Siriya ta yi luguden wuta kan 'yan tawaye
Dakarun Siriya sun yi lugaden wuta kan wani kauye da ke hannun 'yan tawaye a arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu dalibai.

Kauyen na Maaret al-Naasan da ke lardin Idlip mai al'umma fiye da miliyan uku na kansancewa yanki na karshe da 'yan tawayen kasar ke da karfin iko. Kungiyar kare hakkin bil adama ta Siriya da ke da mazauni a Birtaniya ta ce dukkanin daliban da suka gamu da ajalinsu maza ne wadanda shekarunsu bai wuce 18 ba.  

Luguden wutan na wannan Litinin din na zuwan ne yayin da Rasha ta kaddammar da wasu jerin hare-hare a yankin Idlip. Dama dai tun a watan Satumbar shekarar 2015 ne kasar Rasha ke bai wa sojojin shugaba Bashar Assad goyon baya tare da kaddamar da hare-hare ta sama kan yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Kasar Siriya dai ta fada rikici tun a shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane dubu 500 yayin da kimanin rabin al'ummar kasar miliyan 26 suka rasa matsugunnansu.
 


News Source:   DW (dw.com)