A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, ma'aikatar harkokin waje da ta tsaron Siriya sun sanar da shirinsu na cewa askarawan kasar za su yi aiki kafada da kafada da Majalisar Dinkin Duniya wajen tabbatar da tsaron yankin Tddan Golan a Kudu maso yammacin Siriya.
Karin bayani: Isra'ila za ta maida martani kan hari daga Labanan
Bayan karbe iko da ma korar gwamnatin Bachar al-Assad, Isra'ila ta mamaye yankin Tudan Golan bisa abin da ta kira fargabar abubuwan da ka iya-je-su-zo, sannan ta rika yi wa dakarun Siriyar ruwan bama-bamai akai-akai a wata manufa ta rage kaifin karfinsu.
Karin bayani:Isra'ila ta ce tana taimaka wa dakarun MDD a Siriya
Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce mamaye yankin da Isra'ilar ta yi, ya saba yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin bangarorin biyu shekaru 51 da suka gabata.