Sierra Leone ta ayyana dokar ta baci a kasar sanadiyyar annobar cutar kyandar birrai ta mpox, a wani mataki na dakile yaduwarta ta hanyar sintiri da rangadin kula da kan iyakokinta, bayan bullar rahoton kamuwar mutane biyu da cutar, kamar yadda ministan lafiyar kasar Austin Demby ya tabbatarwa manema labarai a birnin Freetown.
Karin bayani:Najeriya ta bai wa Rwanda alluran rigakafin cutar kyandar biri
A ranar 6 ga wannan wata na Janairu ne aka samu mutum na biyu da ya kamu da cutar kyandar birrai a Sierra Leone, bayan ganin alamunta a jikin wani matashi mai shekaru 21, in ji hukumar kula da lafiya ta kasar.
Karin bayani:Cutar kyandar biri ta mpox ta halaka mutane a kasar Kamaru
Sierra Leone na zama kasar da annobar cutar Ebola ta fi yi wa barna, bayan halaka mutane dubu hudu daga shekarar 2014 zuwa 2016, wannan na daga cikin dalilan daukar matakan gaggawa kan cutar kyandar birrai, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan illolinta a bara.