
Shugabannin kasashen yankin Balkans guda hudu sun isa birnin Kiev cikin jirgin kasa domin jadada goyon bayansu ga shugaba Volodymyr Zelensky a yakin da kasarsa take yi da Rasha.
Wannan ita ce ziyara ta biyu da wasu shugabannin yankin na Balkans ke kai wa a Ukraine da nufin nuna goyon bayansu. Shugaban Kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da ke ziyara a birnin Warsaw na Poland ya so tare da shugabannin kasashen na yankin Balkans su kai ziyarar a Kiev amma sai dai shugaban na Ukraine ya ki amincewa. Saboda zargin da ya yi masa na kawo cikas wajen shigar Ukraine cikin kungiyar tarrayar Turai a lokacin da yake rike da matsayin ministan harkokin wajen Jamus.
News Source: DW (dw.com)