Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, sun isa birnin Tehran inda za su tattauna da shugaban Iran Ebrahim Raisi.
A hukumance dai makasudin ziyarar Putin da Erdogan, shi ne domin duba halin da ake ciki a Syria.
A baya dai kasashen uku sun yi ta tattaunawa a game da rikicin kasar ta Syria, inda Rasha da Iran ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.
Tsawon shekarun kuma da Syria ke fama da yaki, a nashi bangaren Shugaba Erdogan na Turkiyya, goyon bayansa na bangaren masu adawa ne da gwamnatin ta Assad.
Ziyarar ta birnin Tehran dai, ita ce ta biyu da Shugaba Putin na Rasha ke yi tun bayan kaddamar da yaki da ya yi a kan kasar Ukraine cikin watan Fabrairu.
Duk da cewa dai babu batun yakin na Ukraine a ajandar taron, ana dai ganin ta yiwu shugabannin su dubi batun a lokacin ganawar tasu a yau Talata.